Hajj 2024: Gwamnoni bakwai da suka bai wa maniyyata tallafi a Najeriya

Date:

Share post:

Asalin hoton, Getty Images

Bayani kan maƙalaMarubuci, Usman MinjibirSanya sunan wanda ya rubuta labari, Senior JournalistAiko rahoto daga Abuja

Sa’a 1 da ta wuce

Da misalin karfe 12 na daren yau ne dai hukumar alhazan Najeriya ta rufe karbar cikon kudin aikin hajjin bana, bayan karin kwanaki hudu da hukumar ta yi a kan ranar rufewar ta farko ta 12 na daren Juma’a ta 29 ga watan Maris.

Kawo yanzu dai jihohi bakwai ne suka bai wa alhazan jihohin nasu tallafin kudi domin rage musu radadin yawan kudaden kujerar aikin hajjin bana da hukumar ta Alhazai ta Najeriya ta sanya.

Hukumar dai ta nemi alhazan da su cika naira miliyan 1.9 kari a kan naira miliyan 4.9 da suka ajiye, inda gabadaya kudin zai kama naira miliyan 6.8 ga maniyyatan da suka kwashe lokaci suna ajiya.

To sai dai kuma sabbin masu son zuwa aikin hajjin za su biya fiye da naira miliyan 8.2 daga arewacin Najeriya, inda takwarorinsu na kudancin kasar za su biya naira miliyan 8.4.

Tundai bayan sanarwar ta hukumar alhazai, ‘yan Najeriya musamman maniyyata suka fara kokawa, inda da dama suka fara cewa “sun hakura da aikin hajjin na bana domin ba dole ne ba ne.”

To sai dai kuma wasu gwamnonin jihohi bakwai sun magantu da kiraye-kirayen da aka yi ta yi musu cewa su bai wa manaiyyatan tallafi, inda suka sanar da ko dai ba su wani kaso ko kuma biya musu kudin gabadaya.

Jihar Kogi ce kadai ta fita zakka inda maniyyatan jihar baki dayansu suka yi abin da ake kira adashin gata kuma tuni suka biya cikakkun kudin nasu.

Ga jerin sunayen gwamnoni da jihohinsu da kuma kudin da suka bai wa maniyyatan.

Kano – Abba Kabir Yusuf

Asalin hoton, Abba Kabiru Facebook

Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf wanda aka fi sani da Abba Gida-Gida shi ne gwamnan jihar da ya fara bayyana tallafin naira dubu 500 ga kowane maniyyaci a jihar.

Abba Kabir ya ce kowane maniyyaci daga cikin maniyyatan jihar 2,906 zai samu naira dubu 500 din.

Kiyasi ya nuna jihar za ta kashe wa alhazan 2,906 naira biliyan 1,453.

Yanzu hakan na nufin cewa kowane maniyyaci daga Kano zai cika naira miliyan 1.4 maimakon naira miliyan 1.9 bayan tallafin gwamnan na Kanawa.

Rivers – Siminalayi Fubara

Asalin hoton, Rivers Media

Shi kuwa gwamnan jihar Rivers da ke kudu maso kudancin Najeriya, Siminalayi Fubara ya sanar da cikasa baki daya cikon kudin wato naira miliyan 1.9 ga alhazan jihar 42.

Sannan ya kuma sayi karin kujeru ga wasu sabbin maniyyatan jihar, wani mataki da Musulman jihar suka yaba.

Jihar River ita ce kadai daga jihohin kudancin Najeriya da ta bai wa mahajjatan tallafi a bayyane, sannan kuma ita kadai ce jihar da ta biya wa maniyyatan cikon kudin gabadaya.

Jigawa – Umar Namadi

Asalin hoton, Jigawa Govt House

Gwamnan jihar Jigawa, Malam Umar Namadi ya bi sahun takwarorinsa gwamnoni wajen bai wa maniyyatan tallafi , inda ya amince zai cika wa kowane maniyyaci daga jihar tasa naira miliyan daya daga cikin naira miliyan 1.9 da hukumar alhazai ta nemi su cikasa.

Dama dai jihar ta Jigawa a baya ta bai wa hukumar alhazan jihar rancen tsabar kudi fiye da naira biliyan biyu domin samun damar sayen kujerun da aka kebewa ‘yan jihar.

Kebbi – Mohammed Nasir Idris

Kamar jihar Jigawa, shi ma gwamnan jihar Kebbi da ke arewa maso yammacin Najeriya ya sanar da cikasawa maniyyatan na bana naira miliyan daya.

Gwamnan ya amince da fitar da tsabar kudi har naira biliyan 3.34 domin cikasa wa maniyyatan jihar su 3,344.

Yanzu kowanne maniyyaci daga jihar ta Kebbi zai cika naira dubu dari tara ne maimakon naira miliyan 1.9.

Sokoto – Ahmad Aliyu

Makwabciyar jihar ta Kebbi wato Sokoto, ita ma ba a bar ta a baya ba wajen tabbatar da cewa maniyyatanta ba su zama cikin wadanda ba za su iya biyan kujerar aikin hajjin bana ba.

Wata majiya a hukumar alhazan Najeriya ta shaida wa BBC cewa gwamna Ahmed Aliyu ya sanar da naira miliyan daya ga kowanne maniyyaci daga cikin maniyyatan jihar su 3,563.

Kafin nan dama sai da gwamnan ta bakin shugaban hukumar alhazan jihar ta Sokoto ya nemi da a kara lokacin rufe karbar kudin aikin hajjin na bana domin gwamnan ya samu zarafin bayar da cikon.

Yobe – Mai Mala Buni

Asalin hoton, Mai Mala Facebook

Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni kamar sauran jihohin kasar ya cikawa maniyyatan jihar naira miliyan daya ga kowanne kamar yadda wata majiya a hukumar alhazan Najeriya ta shaida.

Jihar Yobe dai na da yawan maniyyata 1,290 a 2024.

Bauchi – Bala Muhammad

Asalin hoton, Bauchi govt house

Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed ya amince da fitar da tsabar kudi har naira biliyan 2.1 domin bai wa maniyyatan jihar tallafin naira 959,000 ga kowanne maniyyaci.

Jihar Bauchi dai na daya maniyyata 2,290 kuma hakan na nufin yanzu kowane maniyyaci zai cika naira 950,000 bayan biyan kaso 50 da gwamnatin jihar tasu ta yi.

Jadawalin maniyyata daga jihohi

Kaduna — 4,656Sokoto — 3,563Kebbi — 3,344Niger — 3,200Kwara — 3,100Kano — 2,906Katsina — 2,654FCT — 2,489Bauchi — 2,290Nasarawa — 1,866Lagos — 1,857Borno — 1,780Adamawa — 1,767Zamfara — 1,596Osun — 1,548Plateau — 1,345Yobe — 1,290Gombe — 1,262Jigawa — 1,260Oyo — 1,047Taraba — 1,000Ogun — 925Ondo — 491Edo — 265Ekiti — 186Imo — 98Benue — 87Rivers — 42Delta — 40Enugu — 18Bayelsa — 13Ebonyi — 13Kogi — 13Sojoji — 403

Bisa la’akari da jadawalin da ke sama, Najeriya na da yawan maniyyata 48,414 a shekarar nan ta 2024, sabanin a baya inda ko a 2023 ‘yan Najeriya fiye da dubu 90 ne suka halarci aikin hajjin bara.

Ana dai alakanta raguwar yawan jama’ar da tsadar farashin kujerar aikin na bana da ta ninka na bara fiye da sau biyu.

To sai dai za a iya cewa babu tabbacin cewa gabadayan maniyyatan fiye da dubu 48 na Najeriya ka iya halartar aikin hajjin bana sakamakon ba kowa ne zai iya cika kudin da hukumar alhazan ta nemi a cika duk kuwa da cewa wasu jihohin sun cika wani kaso na kudin.

Yanzu dai za a iya cewa alkaluman da hukumar alhazai za ta fito da su ne kawai ka iya zama abin dogaro dangane da sanin hakikanin yawan mutanen da za su halarci aikin hajjin na 2024.

Related articles

Saudi Ministry of Islamic Affairs Showcases Ancient Manuscripts at Jusoor in Casablanca

Spain's left-wing government said this week it would scrap a national prize for bullfighting, a move which angered...

Awqaf Ministry launches project to build Islamic education centre for girls in Al Waab

Minister of Awqaf and Islamic Affairs H E Ghanem bin Shaheen Al Ghanem (third left) and Director...

Hajj Institute of Nigeria holds Summit on 2024 Hajj – Voice of Nigeria

The Hajj Institute of Nigeria, HIN, will hold its first national stakeholders’ summit on the 2024 Hajj for...