Hajj 2024: Gwamnan PDP Ya Biya Rabin Kuɗin da Aka Ƙarawa Mahajjatan Jihar Arewa, Ya Faɗi Dalili

Date:

Share post:

Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya biya wa kowace mahajjacin jihar rabin kuɗin aikin hajjin bana da aka ƙara kwanan nanKauran Bauchi ya ce ya biya wa dukkan mahajjatan N950,000 daga cikin N1.9m da aka nemi su cika saboda tashin farashin DalaA cewarsa, ya ɗauki wannan matakin ne duba da halin matsin rayuwar da ake fama da shi a faɗin Najeriya

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al’amuran yau da kullum

Jihar Bauchi – Biyo bayan karin da aka samu a kudin kujeran zuwa sauke farali, Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi ya tallafawa dukkan alhazan jiharsa.

Gwamna Muhammed ya amince zai biya kaso 50% na karin ga kowane mahajjaci na jihar Bauchi da ke Arewa maso Gabashin Najeriya, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Musulmai na murna yayin da gwamna Kirista ya biya cikon kudin kujerun Hajji ga maniyyata

Gwamnan Bauchi ya tallafawa mahajjatan bana a jiharsa
Hoto: Senator Bala A. Mohammed
Asali: Facebook

A wata sanarwa da ya fitar ranar Jumu’a, 29 ga watan Maris, 2024, Gwamnan ya ce ya biya rabin ƙarin kuɗin da aka yi kwanan ne sabida halin matsin tattalin arzikin da ake ciki a ƙasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Na biya Naira 950,000 ga kowane mahajjaci na jihar Bauchi, wato kashi 50% na karin kudin da aka samu kwanan nan.”Na kuma umurci hukumar jin daɗin alhazai a matakin jiha da ta mayar wa maniyyata kudaden da muka ba su tallafi, kuma ta karɓi na wadanda ba su biya nasu ba kafin cikar wa’adin.”

– In ji Gwamna Bala Muhammed.

Yadda NAHCON ta ƙara kuɗin Hajji

Wannan na zuwa ne kusan mako ɗaya bayan hukumar alhazai ta ƙasa (NAHCON) ta sanar da ƙarin N1,918,032.91 a kudin sauke farali na wannan shekarar 2024.

A wata sanarwa da mai magana da yawun NAHCON, Fatima Sanda Usara ta fitar, ta ce kowane maniyyaci ya tabbata ya cika waɗannan kuɗin kafin ranar 28 ga watan Maris (jiya).

Kara karanta wannan

Jerin jihohin Najeriya da suka ba alhazai tallafin kudin aikin Hajji

Ta kuma bayyana cewa an samu ƙarin ne sakamakon hauhawar farashin Dala wanda Najeriya ta yi fama da shi na tsawon watanni, rahoton Tribune.

Jihohin da suka bai wa mahajjata tallafi

A wani rahoton kuma kun ji cewa Gwamnonin jihohin Kano, Kebbi da Kogi sun bayar da tallafin kudin Hajji ga maniyyata a jihohinsu.

Matakin dai ya zama wajibi ne biyo bayan karin kudin da hukumar aikin Hajji ta Najeriya ta yi wa alhazan kasar.

Asali: Legit.ng

Related articles